logo

HAUSA

Xi ya duba shirye-shiryen wasannin Olympics na Beijing na 2022

2022-01-05 09:51:50 CRI

Xi ya duba shirye-shiryen wasannin Olympics na Beijing na 2022_fororder_220105-yaya-Xi Jinping

Jiya ne, shugaban Sin Xi Jinping ya duba shirye-shiryen wasannin Olympics da na nakasassu na shekarar 2022 da za su gudana a nan birnin Beijing

Xi, shi kuma babban sakataren kwamitin tsakiya na JKS, ya ziyarci babban zauren wasan zamiyar kankara na kasa da ake kira Oval Skating, da cibiyar watsa labaru, da kauyen 'yan wasa, da cibiyar bayar da umarni na lokacin wasanni, da cibiyar horar da wasanni ta lokacin sanyi, da koyon aikin shirya wasannin, da kuma shirye-shiryen 'yan wasan kasar Sin na shiga wasannin.

Haka kuma Xi ya mika gaisuwar sabuwar shekara ga 'yan wasa, da masu horar da 'yan wasa, da masu aikin sa kai, da wakilan kungiyoyin gudanar da ayyuka, da kafofin yada labarai da ma'aikatan binciken kimiyya.

Za a gudanar da wasannin Olympics na lokacin sanyi na 2022 daga ranar 4 zuwa 20 ga watan Fabrairu, sai kuma wasannin nakasassu daga ranar 4 zuwa 13 ga Maris. (Ibrahim Yaya)