logo

HAUSA

Shugaban Falasdinawa: Dole ne a bude sabuwar hanyar siyasa don kawo karshen mamayar Isra'ila

2022-01-04 14:22:47 CRI

Shugaban Falasdinawa: Dole ne a bude sabuwar hanyar siyasa don kawo karshen mamayar Isra'ila_fororder_220104-Falasdinu-Ibrahim

Kamfanin dillancin labarai na Xinhua, ya ruwaito daga shafin sadarwa na yanar gizo na WAFA cewa, shugaban Falasdinawa Mahmud Abbas ya ce, dole ne a bude sabuwar hanyar siyasa domin kawo karshen mamayar da Isra'ila ke yi.

WAFA ta hakaito Abbas yana fadar haka a karshen taron kwanaki biyu da majalisar juyin juya halin jam’iyyar Fatah ta shirya. Ya kara da cewa, ba za su amince su ci gaba da zama a karkashin mamayar Isra’ila ba, kuma dole ne a kawo karshen mamayar bisa kudurin kasa da kasa da kuma laimar kungiyar Quartet ta kasa da kasa. (Ibrahim Yaya)

WAFA ta hakaito Abbas yana fadar haka a karshen taron kwanaki biyu da majalisar juyin juya halin jam’iyyar Fatah ta shirya. Ya kara da cewa, ba za su amince su ci gaba da zama a karkashin mamayar Isra’ila ba, kuma dole ne a kawo karshen mamayar bisa kudurin kasa da kasa da kuma laimar kungiyar Quartet ta kasa da kasa. (Ibrahim Yaya)Kamfanin dillancin labarai na Xinhua, ya ruwaito daga shafin sadarwa na yanar gizo na WAFA cewa, shugaban Falasdinawa Mahmud Abbas ya ce, dole ne a bude sabuwar hanyar siyasa domin kawo karshen mamayar da Isra'ila ke yi.