logo

HAUSA

A shekarar 2021 yayayin ingancin iska a Beijing ya kai mataki mafi kyau a karon farko

2022-01-04 11:25:12 CRI

A shekarar 2021 yayayin ingancin iska a Beijing ya kai mataki mafi kyau a karon farko_fororder_220104-Iska-Ahmad

A yau, rahoto daga taron ’yan jaridu kan batun yanayin ingancin iska a Beijing a 2021 ya nuna cewa, a shekarar 2021, ta hanyar yin kokari na hadin gwiwa na dukkan bangarori na birnin, yayin da aka ci gaba da samun ingantuwar yanayin iska a birnin da kuma cikakken ingancin yanayin da aka samu fiye da yadda aka saba gani, adadin gurbatacciyar iskar da ake shaka wato (PM2.5) a muhallin Beijing ta ragu zuwa ma’aunin micrograms 33, kuma dukkan adadin gurbatacciyar iskar PM2.5 da kurar iskar ozone wato (O₃), sun kai mataki mafi inganci a lokaci guda. Ya zuwa yanzu, yanayin ingancin iska a Beijing ya riga ya kai mataki mafi inganci a karon karfo. An cimma nasarar shirin takaita fitar da iskar mai gurbata muhalli, kuma wannan muhimmin tarihi ne da aka kafa na shirin takaita fitar da iska mai gurbata muhalli. (Ahmad)