logo

HAUSA

Wakilin musamman na MDD ya bayyana damuwa kan dambarwar siyasar da ake fama da ita a Sudan

2022-01-04 10:06:09 CRI

Wakilin musamman na MDD ya bayyana damuwa kan dambarwar siyasar da ake fama da ita a Sudan_fororder_220104-Sudan-Ibrahim

Wakilin musamman na babban sakataren MDD a kasar Sudan Volker Perthes, jiya Litinin, ya bayyana damuwarsa kan rikicin siyasa da ake fama da shi, da kuma asarar rayukan fararen hula, a zanga-zangar da ’yan kasar ke yi a kan titunan kasar.

Perthes ya bukaci jami'an tsaro, da su mutunta hakkinsu karkashin dokokin kasa da kasa, da kare hakkin masu zanga-zanga na 'yancin fadin albarkacin baki, da gudanar da taro cikin lumana. Yana mai cewa, dole ne a gurfanar da masu aikata laifuka a gaban kuliya.

A jiya litinin ne, shugaban majalisar kolin mulkin Sudan Abdel Fattah Al-Burhan, ya jaddada bukatar kafa gwamnati mai cin gashin kanta tare da amincewar dukkanin al'ummar Sudan, bayan da Abdalla Hamdok ya yi murabus.

Al-Burhan ya jaddada wajibcin cimma muhimman abubuwan dake kunshe cikin shirin mika mulki, da samar da zaman lafiya da tsaro da kuma gudanar da zabuka a kasar.

Sudan dai ta tsunduma cikin rikicin siyasa ne, tun bayan da Al-Burhan, wanda kuma shi ne babban kwamandan sojojin kasar Sudan, ya ayyana dokar ta baci a ranar 25 ga watan Oktoba tare da rusa majalisar koli da gwamnatin kasar. (Ibrahim Yaya)