logo

HAUSA

Burin Sinawa A 2022: Fata Na Gari Lamiri

2022-01-04 17:00:10 cri

Burin Sinawa A 2022: Fata Na Gari Lamiri_fororder_1

Yayin da aka shiga sabuwar shekarar 2022 a karshen makon jiya, al’ummun kasashen duniya sun bayyyana ra’ayoyinsu game da yadda al’amurra suka wakana a shekarar da ta gabata, kamar daga abubuwan farin ciki, da na bakin ciki, da nasarori, da akasin hakan, har ma da burin da ake son cimmawa a sabuwar shekarar ta 2022. Shugabannin kasashen duniya da dama sun yi tsokaci game da fatan da suke da shi a sabuwar shekarar da kuma burikan da suke son cimmawa don kyautata makomar rayuwar al’ummunsu gami da bunkasa ci gaban kasarsu. Tun a jajibiren sabuwar shekarar ta 2022, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya kuma gabatar da jawabin murnar sabuwar shekara, ta babban gidan rediyo da telabijin na kasar Sin CMG, da kuma yanar gizo. Shugban ya ce, shekarar 2021 da aka ga karshenta tana da ma’ana ta musamman, saboda an ga wasu abubuwa masu ma’ana a tarihi dangane da kasar ta Sin, da jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin dake rike da ragamar mulkin kasar. Yanzu haka ana kokarin cimma buri na gina al’umma mai walwala, da raya kasa da gina ci gaban kasar mai bin tsarin gurguzu a sabon zamanin da muke ciki. Shugaban ya ce, a cikin shekarar da ta gabata, an saurari muryar kasar Sin, da labaran kasar Sin, masu burgewa. Ko shakka babu, duniya ta amfana da irin ci gaban da kasar Sin ta samu, musamman a kokarinta na kara zurfafa bude kofarta ga ketare, da karfafa hadin gwiwarta da kasa da kasa, musamman karkashin tsarin MDD, da yadda kasar ta tsaya tsayin daka wajen yin hadin gwiwa da sauran kasashen duniya don yaki da annobar COVID-19, da samar da tallafin kiwon lafiya ga kasashe da dama musamman kasashe masu tasowa. Alkaluma sun nuna cewa, ya zuwa karshen watan Disambar shekarar 2021, kasar Sin ta samarwa kasashen duniya da hukumomin kasa da kasa 120 riga-kafin cutar numfashi ta COVID-19 sama da biliyan 2. Shugaban na kasar Sin ya ce ana sa ran samun ci gaba mai armashi nan gaba tare da nuna fatan alheri ga samun bunkasuwar kasa da kyautatuwar zaman rayuwar jama’a nan gaba.
Shi ma a nasa kalaman, ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi ya ce, a sabuwar shekarar gargajiyar Sin ta Damisa, Sin za ta ci gaba da dora muhimmanci ga kare manyan moriyarta, za ta kuma ci gaba da yin hadin gwiwa da sauran sassan duniya wajen wanzar da zaman lafiya da ci gaba mai karsashin irin na Damisa, kuma kasar za ta ingiza manyan nasarori na ci gaban bil adama. Wang Yi ya bayyana hakan ne yayin zantawarsa da kafar CMG, a jajibiren shiga sabuwar shekarar 2022, inda ya ce, Sin na adawa da matakan nuna danniya, tana kuma sauke nauyin dake bisa wuyanta a fannin diflomasiyyar kasa da kasa. A bangaren tattalin arziki kuwa, Wang ya ce a shekarar 2022, Sin za ta ci gaba da ingiza tasirinta a fannin samar da hajojin masana’antu na bukatun yau da kullum, tare da hada karfi da kasashen yankin wajen bunkasa hada hadar tattalin arziki domin cin moriyar juna. Kamar dai yadda masu hikimar magana ke cewa, “fata na gari lamiri.”