logo

HAUSA

Kasar Sin na shirin kaddamar da ayyukan zuwa bangaren kudancin duniyar wata

2022-01-04 11:06:29 CRI

Kasar Sin na shirin kaddamar da ayyukan zuwa bangaren kudancin duniyar wata_fororder_220104-wata-Ibrahim

Hukumar binciken sararin samaniya ta kasar Sin ta bayyana cewa, kasar ta amince da kashi na hudu na shirin binciken duniyar wata, ciki har da wani muhimmin tsari na tashar bincike da aka gina kan duniyar wata cikin shekaru 10 masu zuwa.

Mataimakin daraktan hukumar Wu Yanhua ya bayyana cewa, kasar Sin za ta gudanar da aikin binciken duniyar wata a nan gaba a ayyukan Chang'e-6 da Chang'e-7 da kuma na Chang'e-8.

Kamar yadda aka tsara, za a fara kaddamar da aikin harba na’urar Chang'e-7 zuwa sashen kudancin duniyar wata. Tun da na’urar Chang'e-6 ta maye gurbin aikin dawo da samfura da Chang'e-5 ta gudanar, za a kaddamar da ita bayan Chang'e-7 ta dawo da samfura daga bangaren kudancin duniyar wata. Haka kuma aikin harba na’urar Chang'e-6, zai biyo bayan na Chang'e-8, wani muhimmin mataki na aikin gina samfurin tashar binciken kimiyyar duniyar wata.

Wu ya bayyaya yayin wata hira da aka yi da shi a baya-bayan nan cewa, kasar Sin ta shirya yin aiki tare da kasar Rasha, don gina ainihin samfurin tashar binciken duniyar wata. Yana mai cewa, gina tashar zai kafa ginshiki mai inganci, don kara nazarin yanayin duniyar wata, da albarkatun kasa, gami da yadda ake amfani da kuma bunkasa albarkatun duniyar wata cikin lumana. (Ibrahim)