logo

HAUSA

Kasar Sin ta yabawa sanarwar hadin gwiwa kan tsaron nukiliya ta zaunannun mambobin kwamitin sulhun MDD

2022-01-04 11:32:47 CRI

Kasar Sin ta yabawa sanarwar hadin gwiwa kan tsaron nukiliya ta zaunannun mambobin kwamitin sulhun MDD_fororder_220104-nuclear-Ahmad

Mataimakin ministan harkokin wajen kasar Sin Ma Zhaoxu, a ranar Litinin ya yabawa sanarwar hadin gwiwar da shugabannin kasashe biyar na makaman nukiliya, wato Sin, Faransa, Rasha, Birtaniya da Amurka suka fidda game da daukar matakan dakile yakin makaman nukiliya da kuma kaucewa daukar makaman yaki.

Cikin sanarwar, kasashen biyar sun jaddada cewa, babu guda daga cikinsu dake da burin afkawa makaman nukiliyar kowannensu, ko ma sauran kasashen duniya, kuma ba za a taba cimma nasarar yakin makaman nukiliya ba, kana tilas ne a kaucewa faruwar fadan.

A yayin wata tattaunawa, Ma ya bayyana cewa, wannan shi ne karon farko da shugabannin kasashen biyar suka fidda sanarwa kan batun makaman nukiliyar, kuma hakan ya nuna irin matakan siyasar da suka dauka wajen hana barkewar yakin makaman nukiliya, hakan ya kuma isar da wani sako game da dabarun tabbatar da zaman lafiyar duniya da kuma rage barzanar yakin makaman nukiliya a duniya.

Ya ce, sanarwar ta kuma taimakawa kasashen biyar masu wakilcin dindindin a kwamitin sulhun MDD wajen kara amincewa da juna da kuma maye gurbin takarar neman karfin fada a ji ta hanyar karfafa hadin gwiwarsu. (Ahmad)