logo

HAUSA

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Sin: Sin za ta hada kai tare da sauran kasashe don samar da makoma mai haske

2022-01-04 21:23:12 CRI

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Sin: Sin za ta hada kai tare da sauran kasashe don samar da makoma mai haske_fororder_1

Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin, ya bayyana a yau Talata cewa, a sabuwar shekarar da muke ciki, za’a gudanar da harkokin diflomasiyyar kasar Sin bisa jagorancin tunanin Xi Jinping, da tsayawa haikan, kan ra’ayin gina al’umma mai kyakkyawar makoma ta bai daya, da mayar da muradun al’umma a gaban komai, da ci gaba da nuna himma da kwazo wajen daukar matakai a zahiri, domin kirkiro muhalli mai kyau wajen farfado da al’ummar kasar, da yin kokari tare da kasashe daban-daban, don samar da makoma mai haske ga daukacin al’umma. (Murtala Zhang)