logo

HAUSA

Kwalliya ta biya kudin sabulu a kokarin da kasar Sin ke yi na inganta muhalli

2022-01-03 22:21:07 CRI

Kwalliya ta biya kudin sabulu a kokarin da kasar Sin ke yi na inganta muhalli_fororder_fd039245d688d43f79dc7f823e6e611e0ef43b3b

“Tun daga farkon shekarar 2021, har zuwa karshenta, jama’ar kasarmu suna ta hidima a cikin gonaki, da kamfanoni, da ungwanni, da makarantu, da asibitoci, da sansanonin soja, da cibiyoyin nazarin kimiya da fasaha. A kokarin samar da gudunmawa, da cimma dimbin nasarori, a wannan shekara mun ga yadda kasar Sin take kara samun ci gaba, ta hanyar jajircewa.” Kamar yadda aka saba, a jajebirin sabuwar shekara ta 2022, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar da jawabi, don isar da gaisuwar sabuwar shekara ga al’ummun cikin gida da na ketare, inda kuma ya waiwayi al’amuran da suka wakana cikin shekarar 2021 da aka ga karshenta.

Babu shakka, shekarar 2021 tana da ma’ana ta musamman. A shekarar, jam’iyyar kwaminis mai mulkin kasar Sin ta cika shekaru 100 da kafuwa, kasar Sin ta kuma cimma nasarar gina zaman al’umma mai matsakaicin karfi.

A jawabinsa, shugaba Xi Jinping ya ce, “A tarihin kasar Sin, al’ummun Sinawa suna sa ran kiyaye tsaron Rawayen kogin, a cikin ’yan shekarun da suka gabata, na ziyarci jihohi tara da kogin ya ratsa, ko Rawayen kogi, ko kogin Yangtse, wadanda aka mayar da su matsayin mahaifiyar al’ummun Sinawa, ko tafkin Qinghai, ko kogin Yarlung Zangbo, ko babban aikin sauya hanyar ruwa daga kudu zuwa arewa, ko gandun daji na Saihanba, ko yawon giwaye daga kudu zuwa arewa a lardin Yunnan, da komawarsu inda suka fito, ko kaurar gadar jihar Tibet, duk wadannan sun nuna cewa, idan bil adama ya yi kokarin kiyaye muhalli, to tabbas za a cimma burin da aka sanya gaba.” Abun hakan yake. A shekarar da ta gabata, ra’ayin kiyaye muhalli ya kara zaunar da gindinsa a zukatan jama’ar kasar Sin, kuma an cimma sabbin nasarori wajen kiyaye da inganta muhalli a kasar Sin, matakin da ya samar da himma da karfi ga aikin inganta muhalli a fadin duniya.

A shekarar 2021, ban da yawon giwaye daga kudu zuwa arewa a lardin Yunnan na kasar Sin, da komawarsu inda suka fito, yawan dabbobin panda ma sun karu a kasar, a yayin da nau’in tsuntsu da ake kira Crested Ibis wanda guda 7 ne kacal a farkon lokacin da aka gano su, yanzu sun karu zuwa 5000……

A shekarar 2021, kasar Sin ta gaggauta gina tsarin gandun daji, inda ta kafa jerin gandun daji a matakin kasa. Dazuzzuka sun game sama da kaso 23% na fadin kasar, baya ga kuma sassan kiyaye muhalli kimanin dubu 11.8 da aka kafa, don haka kuma, kasar ta zama kasar da ta fi samun karuwar fadin dazuzzuka a yankin Asiya da tekun Pasifik.

A shekarar 2021, an kaddamar da cinikayya a kasuwar hakkin fitar da hayakin Carbon Dioxide ta kasar Sin, a yayin da yawan wutar lantarki da aka samar ta amfani da makamashi mai tsabta ya zarce KW triliyan daya a kasar, kuma yawan motoci masu aiki da sabon makamashi da aka sayar ma sun kafa sabon tarihi. Manufar kiyaye muhalli ta kuma sa kaimin faruwar sauye sauye ga zaman takewar al’ummar kasar Sin.

A shekarar 2021, kasar Sin da muhallinta ke dinga inganta, ta kuma yi kokarin samar da gudummawarta ga aikin kiyaye muhalli a fadin duniya. A birnin Kunming, hedkwatar lardin Yunnan na kasar, an gudanar da babban taro karo na 15, na mambobin kasashen da suka kulla yarjejeniyar kiyaye mabambantan halittu ta duniya wato COP15, inda aka zartas da sanarwar Kunming, don yin kira ga bangarori daban daban, da su dauki matakai na kiyaye yanayin halittu a duniya.

Baya ga haka, kasar Sin ta kuma hada gwiwa tare da kasashe 28 da suka amince da shawarar ziri daya da hanya daya, wadanda suka gabatar da shawarar samar da ci gaba ba tare da gurbata muhalli ba, tare da aiwatar da shirin hadin gwiwar kasashe masu tasowa wajen tinkarar sauyin yanayi karkashin shawarar ziri daya da hanya daya……

Idan dai bil adama ya yi kokarin kiyaye muhalli, to tabbas za a cimma burin da aka sanya gaba. A cikin sabuwar shekara, kasar Sin za ta ci gaba da kokarinta na kiyayewa da inganta muhalli, tare da samar da karin taimako a aikin kiyaye muhalli a fadin duniya.(Lubabatu)