logo

HAUSA

Wane hali dubun dubatar iyalai Sinawa ke ciki a kasar

2022-01-03 21:53:29 CRI

Wane hali dubun dubatar iyalai Sinawa ke ciki a kasar_fororder_1

Mai yiwuwa wani ya yi tambaya kan yanayin da dubun dubatar iyalai Sinawa suka kasance a shekarar 2021? Mece ce damuwarsu, kuma wadanne matsaloli suke fuskanta?

Duk inda ya ziyarta, shugaban kasar Sin Xi Jinping na nuna kulawarsa. Ya kan ce: "Idan na je wurare, na kan ziyarci yankunan karkara, da inda al’umma ke rayuwa, domin ganin yadda jama’ar mu suke." "babban burin mu shi ne ganin al’umma na rayuwa cikin farin ciki".

A shekarar 2021, daya daga manyan matsaloli da ilimin wajibi ya fuskanta, shi ne nauyin ayyukan dalibta da ke kan daliban firamare da sakandare, wanda hakan ya sa shugaba Xi Jinping ya jaddada cewa: "Ya kamata mu aiwatar da dukkanin manufofin ilimi na jam’iyya, mu aiwatar da ginshikan aikin kafa da’a da renon al’umma, mu yi riko da ka’idojin kyautata samar da ilimi ga al’umma, da zurfafa gyare gyare a fannin ilimi, da gudanar da tsarin ilimi da zai gamsar da al’umma." Bisa hake ne kuma, nan da nan, gwamnatin kasar Sin ta kaddamar da wani tsari na ragewa yara ‘yan makaranta yawan ayyukan gida na karatu, da sauran horo da ake wajabta musu yi a gida, yayin da suke halartar ilimin wajibi.

A shekarar 2021, cutar Covid-19 ta rika kwan-gaba kwan-baya cikin sauri, nau’o’in ta sun rika canzawa, kuma har yanzu matakan kandagarki da na shawo kan annobar suna kunshe da sarkakiya. Kan haka, shugaban na Sin ya ba da umarnin aiwatar da matakan kandagarki, da na shawo kan annobar, wanda hakan ya ba da damar cimma manyan nasarori.

A shekarar 2021, bisa karfin goyon bayan gwamnatin Sin, an aiwatar da matakan gaggawa kuma mafiya dacewa, na samar da hidimar kula da tsofaffi ga iyalansu. Gwamnatin kasar Sin ta samar da kudi har yuan biliyan 1.1, domin tallafawa ayyukan raya hidimomin kula da tsofaffi a gidaje da unguwanni, a yankunan kasar 42, wanda hakan ya dace da yanayin bukatun tsofaffi a kasar. (Saminu)