logo

HAUSA

Yankin hakar mai da iskar gas na Sin ya kafa sabon tarihi

2022-01-03 16:14:56 CRI

Yankin hakar mai da iskar gas na Sin ya kafa sabon tarihi

Yankin hakar mai da iskar gas na Changqing dake kasar Sin, ya kafa sabon tarihin samar da danyen mai da iskar gas, sama da tan miliyan 62.4 a shekarar 2021, adadin da ya karu da sama da tan miliyan 2, da aka haka a wurin a shekarar 2020.

A shekarar 2020, yankin ya kasance na farko a Sin, da ya haura adadin tan miliyan 60, da ake hasashen samu daga makamantansa dake sassan kasar, wanda hakan ya kafa wani sabon tarihi a fannin samar da makamashi a tarihin Sin. Kuma adadin ya kai daya bisa shida, na jimillar mai da iskar gas da ake samarwa a kasar baki daya.

Wurin hakar mai na Changqing, na da tarihin shekaru sama da 50, ya kuma taka muhimmiyar rawa wajen samar da isasshen makamashi a kasar Sin, inda yake samar da gas zuwa sama da birane 50, dake arewaci da arewa maso yammacin kasar.

Yana kuma, ya ba da gudummawa ga shirin kasar Sin na maye gurbin kwal, da nau’o’in makamashi masu tsafta, kamar iskar gas. Yayin da kasar ke fatan kaiwa kolokuwar fitar da iskar carbon mai dumama yanayi nan da shekarar 2030, sannan za ta yi kokarin samun daidaito tsakanin yawan hayakin da za ta fitar, da yawan abubuwan da za su shawo kan hayakin kafin shekarar 2060. (Saminu)