logo

HAUSA

Samar da ci gaba tare da kasa da kasa shi ne ainihin ci gaba

2022-01-03 21:56:23 CRI

Samar da ci gaba tare da kasa da kasa shi ne ainihin ci gaba_fororder_A

Shekara ta 2021, ita ce ta cika shekaru 50 da maidowa Jamhuriyar Jama’ar kasar Sin da halastacciyar kujerar ta a Majalisar Dinkin Duniya, kana ta cika shekaru 20 da shigar kasar WTO wato kungiyar cinikayya ta duniya.

A ranar 14 ga watan Oktobar bara, shugaba Xi Jinping ya halarci bikin bude babban taron sufuri mai dorewa na MDD karo na biyu, inda ya gabatar da jawabin cewa, samar da ci gaba tsakanin kasa da kasa shi ne ainihin ci gaba, kuma samar da wadata tsakanin kowa da kowa ita ce ainihin wadata.

Samar da ci gaba tare da kasa da kasa shi ne ainihin ci gaba_fororder_B

A ranar 25 ga watan Fabrairun bara, an kira babban taron karramawa wadanda suka yi fice a fannin yaki da talauci a kasar Sin, inda shugaba Xi ya sanarwa duk duniya cewa, kasarsa ta cimma babbar nasarar kawar da talauci daga dukkanin fannoni.

Bugu da kari, a wajen shawarwari tsakanin shugabannin Sin da Afirka, da manyan jami’an bangarorin masana’antu da kasuwanci, shugaba Xi ya gabatar da wani jawabi mai taken “kama hanyar samun wadata tare”, inda ya jaddada goyon-bayan kasarsa ga nahiyar Afirka, don halartar ayyukan shawarar “ziri daya da hanya daya”, da samun ci gaba tare. Shugaba Xi ya nuna cewa, samar da ci gaba tare da al’ummomin kasa da kasa, ciki har da al’ummomin Afirka, shi ne muhimmin fanni a aikin gina al’umma mai kyakkyawar makoma ta bai daya.(Murtala Zhang)