logo

HAUSA

Tsayin layukan dogo na jiragen kasa masu saurin tafiya na Sin ya haura kilomita 40,000

2022-01-03 16:18:55 CRI

Tsayin layukan dogo na jiragen kasa masu saurin tafiya na Sin ya haura kilomita 40,000_fororder_W020160215638345824015

Kamfanin dake lura da sufurin jiragen kasa na Sin, ya ce ya zuwa karshen shekarar bara, tsayin layukan dogo na jiragen kasa masu saurin tafiya na Sin ya haura kilomita 40,000.

A ranar Alhamis ne aka bude sashin layin dogo na Anqing zuwa Jiujiang, na jiragen kasa masu saurin tafiya, wanda ya zamo na baya bayan nan cikin jerin wadanda kasar ke amfani da su.

Sakamakon kaddamar da layin dogon, an samu damar hade birnin Hefei babban birnin lardin Anhui, da birnin Nanchang, babban birnin lardin Jiangxi dake gabashin kasar, kai tsaye da jirage masu saurin tafiya. Kazalika nisan tafiya tsakanin biranen biyu zai ragu zuwa sa’o’i 2 da mintuna 22.

Kididdiga ta nuna jimillar tsayin layukan dogo na kasar Sin da ake aiki da su a halin yanzu, ya kai sama da kilomita 150,000.   (Saminu)