logo

HAUSA

Firaministan Sudan ya yi murabus

2022-01-03 15:40:09 CRI

Firaministan Sudan ya yi murabus_fororder_9d82d158ccbf6c815e6fa35ada731d3c32fa40fb

Firaministan kasar Sudan Abdalla Hamdok ya yi murabus a jiya Lahadi, a gabar da kasar ke shan fama da rikicin siyasa. Cikin wani jawabi da ya yi ta kafar talabijin din kasar, Hamdok ya jaddada muhimmancin gudanar da cikakkiyar tattaunawar siyasa, wadda za ta hade daukacin sassa, ta yadda za a kai ga warware matsalolin da ake fuskanta.

Kawo yanzu, ba a tantance wanda zai maye gurbin Hamdok ba, ganin yadda kasar ke fama da rashin tabbas a siyasance, tun bayan da babban kwamandan sojojin kasarAbdel Fattah Al-Burhan, ya kaddamar da dokar ta baci a ranar 25 ga watan Oktoba, inda ya rushe babbar majalissar zartaswar kasar, da ma gwamnatin rikon kwaryar kasar.

A ranar 21 ga watan Nuwamba kuma, Al-Burhan da firaminista Abdalla Hamdok, wanda a lokacin aka tsige daga mukaminsa, suka sanya hannu kan yarjejeniyar siyasa, wadda a cikin ta aka amince ya koma mukaminsa na firaminista. To sai dai kuma, komawar ta sa ba ta dakatar da zanga zangar al’umma ba.

A jiya Lahadi ma, mutane 2 sun rasa rayukan su, yayin zanga zangar da aka yi a birnin Khartoum, kamar dai yadda kungiyar likitocin kasar ta CCSD ta bayyana.

Mutanen biyu sun rasu ne sakamakon harbin bindiga, wanda hakan ya kai adadin wadanda suka rasu sakamakon zanga zangar zuwa mutum 56, tun daga ranar 25 ga watan Oktoban bara, lokacin da dubban ‘yan kasar suka kwarara kan tituna suna neman a koma mulkin farar hula.

Da sanyin safiyar jiya, masu zanga zanga sun taru a tashar shiga motoci ta Sharwani dake birnin Khartoum, suka kuma nufi ginin fadar gwamnati.  (Saminu)