logo

HAUSA

An kammala aikin gina yankin ciniki maras shinge mafi girma a duniya

2022-01-02 16:57:08 CRI

An kammala aikin gina yankin ciniki maras shinge mafi girma a duniya_fororder_1

Jiya Asabar 1 ga watan farko a shekara ta 2022, an fara amfani da yarjejeniyar RCEP, wato yarjejeniyar kawancen raya tattalin arzikin shiyya, al’amarin da ya shaida cewa, an kammala aikin gina yankin cinikayya maras shinge mafi girma a duk fadin duniya. Ana sa ran zuwa shekara ta 2025, yarjejeniyar RCEP za ta taimakawa kasashe membobinta wajen samun karuwar cinikayyar waje, da ajiyar jarin waje, da kuma GDP, da kashi 10.4% da kashi 2.6% da kuma kashi 1.8%.

A nasa bangaren, mai magana da yawun ma’aikatar kasuwancin kasar Sin, Gao Feng ya bayyana cewa, bayan da aka rage kudin haraji, za’a soke harajin kwastam da ake bugawa kan wasu hajojin da kasar Sin take shigowa da su daga kasashen waje, ciki har da lemon kwakwa, da abarba, da kayan takarda da ta shigo da su daga kungiyar ASEAN, da sauran wasu na’urorin aikin injiniya da sassan motoci da dai sauransu. Har wa yau, sannu a hankali za kuma a cire harajin da ake bugawa kan wasu kayayyakin da kasar Sin take fitarwa zuwa kasar Japan, ciki har da na’urorin latironi, da sitiru da albarkatun ruwa da kayan lambu da sauransu. Gao ya kara da cewa, bisa yarjejeniyar RCEP, kamfanonin dake shiyyar za su rage kudaden da suke kashewa wajen yin kere-kere, masu sayayya ma za su iya samun damar sayen kayayyaki masu inganci kuma cikin farashi mai sauki. Bugu da kari, wasu sabbin sana’o’i za su fuskanci karin damammakin ci gaba, ciki har da ciniki da bada ilimi da ganin likita ta yanar gizo, ta yadda al’ummar shiyyar za su iya kara cin alfanu gami samun saukin rayuwa. (Murtala Zhang)