logo

HAUSA

Shugaban kasa: Najeriya ta samu farfadowa mai karfi a 2021 duk da illar annoba

2022-01-02 18:07:54 CRI

Shugaban kasa: Najeriya ta samu farfadowa mai karfi a 2021 duk da illar annoba_fororder_rBABCmDw8vWASVwnAAAAAAAAAAA417.1024x576.200x113

Shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari, ya bayyana a ranar Asabar cewa, kasar mafi karfin tattalin arziki a nahiyar Afrika ta samu farfadowar tattalin arziki mai karfi a shekarar 2021 duk da fuskantar illolin da ake fama da su sakamakon yaduwar annobar COVID-19, yayin da kasar ta samu bunkasuwar tattalin arzikinta a jere ya zuwa yanzu.

Cikin jawabin da shugaban ya gabatarwa ‘yan kasar na murnar sabuwar shekara, shugaba Buhari ya ce, an samu gagarumin ci gaban tattalin arzikin GDPn kasar kamar yadda hukumar kididdiga ta kasar NBS ta bayyana, inda alkaluman suka nuna cewa kasar ta samu karuwar tattalin arziki da kashi 4.03% a rubu’i na uku na shekarar 2021, lamarin da ke nuna karfin farfadowar tattalin arzikin kasar.

Shugaba Buhari ya ce, bunkasuwar da aka samu ta baya bayan nan shi ne karin kashi 5.1% na tattalin arzikin kasar wanda aka samu rubu’i na biyu na shekarar 2021, wanda ya bayyana shi a matsayin bunkasa mafi girma da wata kasa a yankin kudu da hamadar Afrika ta samu, kuma shi ne bunkasar tattalin arziki mafi girma da kasar ta samu tun a shekarar 2014.

Shugaban Najeriyar, ya yi alkawarin karfafa fannin tattalin arziki na zamani a wannan sabuwar shekara, domin samar da karin guranen aiki da tabbatar da fadada karin hanyoyin bunkasar tattalin arzikin kasar da nufin tallafawa sauran hanyoyin tattalin arzikin kasa, don tabbatar da samun cigaba mai dorewa.

Ya ce masu zuba jari daga kasashen ketare suna amfani da damammakin da Najeriya ta samu a matsayin kasar dake sahun gaba, inda suke zuba jarinsu a fannonin tattalin arziki na zamani.(Ahmad)