logo

HAUSA

Sabon ra’ayin samar da ci gaba ya jagoranci aikin raya duk kasar Sin

2022-01-02 21:37:30 CRI

Sabon ra’ayin samar da ci gaba ya jagoranci aikin raya duk kasar Sin_fororder_1

Shekara ta 2021, shekara ce da kasar Sin ta kaddamar da babban aikinta na gina kasa don ta zama kasar zamani mai bin tsarin gurguzu daga dukkan fannoni, inda kasar ta fara aiwatar da shirin raya kasa na shekaru biyar karo na 14.

Sabon ra’ayin samar da ci gaba ya jagoranci aikin raya duk kasar Sin_fororder_2

Shirin ya bukaci a samar da ci gaba mai inganci a fannonin tattalin arziki da rayuwar al’umma, da biyan bukatun al’umma na jin dadin rayuwa, da kuma neman samar da wadata tare.

Sabon ra’ayin samar da ci gaba ya jagoranci aikin raya duk kasar Sin_fororder_3

Shirin ya kuma tsara ajandar hanzarta raya hanyoyin ruwa da na mota gami da gina wasu muhimman ayyuka. Daga watan Janairu zuwa Nuwambar bara, yawan jarin da aka zuba a fannin gina muhimman layukan dogo a duk kasar Sin ya zarce Yuan biliyan 640, kana tsawon sabbin layukan dogon da aka gina ya kai kilomita 1644, kuma tsawon layukan dogo masu saurin tafiya ya zama kan gaba a duk fadin duniya baki daya.

A bara kuma, kasar Sin ta kara yin kirkire-kirkire, da kokarin kiyaye muhallin halittu, da kara bude kofarta ga kasashen waje, inda “sabon ra’ayin samar da ci gaba”ya jagoranci duk kasar wajen shawo kan kalubale da samun bunkasuwa. (Murtala Zhang)