logo

HAUSA

Shugabannin kasashe da na kungiyoyin kasa da kasa sun gabatar da jawaban murna shiga sabuwar shekara

2022-01-02 16:55:45 CRI

Shugabannin kasashe da na kungiyoyin kasa da kasa sun gabatar da jawaban murna shiga sabuwar shekara_fororder_A

A kwanan nan shugabannin kasashe da na kungiyoyin kasa da kasa suka gabatar da jawaban murnar shiga sabuwar shekarar 2022, inda suka yi kira a zama tsintsiya madaurinki daya, domin yakar cutar COVID-19 da haye wahalhalu da kuma kokarin samun farfadowa.

Shugaban kasar Rasha Vladimir Putin ya bayyana cewa, kasarsa ta shawo kan matsaloli da dama a shekarar da ta gabata, ganin yadda al’ummar kasar suka jajirce wajen yin aiki tukuru. Rasha za ta kara bunkasa ayyukan kyautata rayuwar al’umma.

A nasa bangaren, shugaban kasar Kenya Uhuru Kenyatta ya ce, kasarsa za ta kara kula da lafiyar dukkanin al’ummarta a shekara ta 2022, kana, za ta ci gaba da tsayawa kan ra’ayin samar da ci gaba bisa hadin gwiwa tare da sauran kasashe, da mara baya ga harkokin shimfida zaman lafiya da jituwa da neman sulhu da hadin-gwiwa karkashin kwamitin sulhun Majalisar Dinkin Duniya.

Ita ma a nata bangaren, shugabar kasar Tanzaniya Madam Samia Suluhu Hassan ta gabatar da jawabin cewa, a shekarar da ta shude, kasarta ta cimma manyan nasarori a fannoni daban-daban, ciki har da tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali, da habaka tattalin arziki, da neman samun isassun kudaden musanya. Har wa yau, Tanzaniya ta aiwatar da manufofin da suka shafi doka da haraji don kara jawo jarin waje.

Shugaba Macky Sall na kasar Senegal ya bayyana cewa, a sabuwar shekara, gwamnatinsa za ta kara inganta gina muhimman ababen more rayuwar al’umma, da farfado da tattalin arzikin yankunan karkara tare da samar da karin guraban ayyukan yi ga matasa da mata a kasar. (Murtala Zhang)