logo

HAUSA

Shugaban kasar Sin ya mika sakon ta’aziyyar mutuwar tsohon shugaban kasar Girika

2022-01-02 18:17:21 CRI

Shugaban kasar Sin Xi Jinping a ranar Juma’a ya aike da sakon ta’aziyya ga shugabar kasar Girka, Katerina Sakellaropoulou, bisa rasuwar tsohon shugaban kasar Karolos Papoulias.

Xi ya kara da cewa, yana dora muhimmanci game da cigaban huldar dake tsakanin Sin da Girika, kuma a shirye yake yayi aiki tare da Sakellaropoulou don zurfafa muhimmiyar huldar abokantaka dake tsakanin kasashen biyu, da kara ingiza sabbin nasarorin da aka cimma karkashin hadin gwiwa dake tsakanin kasashen biyu daga dukkan fannoni don amfanawa kasashen da kuma al’ummunsu.(Ahmad)