logo

HAUSA

Shugaban Afrika ta kudu ya tuna da wadanda COVID 19 ta yi ajalinsu a cikin jawabinsa na sabuwar shekara

2022-01-01 15:59:04 CRI

Shugaban Afrika ta kudu ya tuna da wadanda COVID 19 ta yi ajalinsu a cikin jawabinsa na sabuwar shekara_fororder_Cyril

Shugaban kasar Afrika ta kudu, Cyril Ramaphosa, ya ce kasar na tunawa da asarar da COVID-19 ta haifar, inda aka yi rashin rayuka da dama saboda annobar a shekarar 2021.

Cyril Ramaphosa ya bayyana haka ne da yake gabatar da jawabin sabuwar shekarar 2022.

A cewarsa, a cikin shekarar, an yi asarar mata da maza dake zaman tubalin al’ummomi, da shugabanni da masu fafutuka da kwararru, wadanda suka yi gwagwarmayar neman ‘yanci.

Ya kuma yi kira ga jama’a su yi amfani da wannan lokaci, wajen ba da gudunmuwar da za su iya ga al’ummominsu.

Zuwa ranar Alhamis, mutane 91,061 ne suka rasa rayukansu sanadiyyar cutar COVID-19 a kasar Afrika ta Kudu. (Fa’iza Mustapha)