logo

HAUSA

Sin: Amurka ta fi yada labaran bogi a duniya

2022-12-30 20:02:23 CMG HAUSA

Kwanan baya, jaridar “New York Post”, da wasu kafofin yada labarai na kasar Amurka sun ruwaito cewa, ma’aikatar tsaron Amurka, da hukumar leken asiri ta kasar wato FBI, suna kirkiro labaran zamba, da juyar da tunanin al’ummar Amurka, da na waje ta hanyar shafunan sada zumunta.

Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin, ya amsa tambaya da aka yi masa a yau a gun taron manema labarai cewa, shaiddun da aka bayar na nuna cewa, Amurka ta baza labaran bogi mafi yawa a duniya, kuma mai fuskoki biyu kan yada labarai cikin ‘yanci.

A cewarsa, labaran da aka bayar na cewa, wani sashin ma’aikatar tsaron Amurka, ya taba kafa masu amfani da Intanet na jabu a Twitter, da tilastawa kamfanin da ya mayar da su cikin sunayen masu amfani da Intanet bisa hanya da ta dace, da mallakar ra’ayoyi kan wasu batutuwa da yin farfaganda ba bisa gaskiya ba, da kuma sarrafa fahimtar jama’ar yankin gabas ta tsakiya, da ma gyara matakan soja da Amurka da kawayenta suka aiwatar a yankin.

Ban da wannan kuma, labaran sun fayyace cewa, gwamnatin Amurka ta taba matsawa kamfanin Twitter lamba bayan barkewar cutar COVID-19, domin kamfanin ya kulle shafukan masu amfani da manhajar wadanda suka sabawa ra’ayin gwamnatin. (Amina Xu)