Kasar Sin ta jaddada bukatar samun ci gaba mai aminci a shekarar 2023
2022-12-29 12:18:00 CMG Hausa
Hukumar kula da raya kasa da aiwatar da gyare-gyare ta kasar Sin, ta jaddada bukatar aiwatar da manufofin tunkarar annobar COVID-19, yayin da ake kyautata daidaito tsakanin ayyukan kandagarki da takaita yaduwar annobar da kuma ayyukan raya tattalin arziki da zamantakewa a shekarar 2023.
Shugaban hukumar He Lifeng, ya bayyana yayin wani taro a jiya Laraba cewa, ya kamata hukumomin raya kasa da aiwatar da gyare-gyare a dukkan matakai a fadin kasar, su himmantu wajen daidaita ayyukan ci gaba da samar da ayyukan yi da daidaita farashin kayayyaki da kuma karfafa kwarin gwiwar kasuwa.
Ya kara da cewa, ya kamata hukumomi su fadada bukatar kayayyaki a gida, su kuma bada dama ga bangaren amfani da kayayyaki da na zuba jari su taka rawar da ya kamata wajen bunkasa ci gaban tattalin arzikin kasar.
Bugu da kari, ya bukaci a yi kokarin kawar da abubuwan dake tarnaki ga samun ci gaba da karfafa dogaro da kai a fannin kimiyya da fasaha. Haka kuma, ya ce ya kamata a gaggauta raya tsarin masana’antu na zamani da samar da tsarin jigila na zamani da kuma kaiwa matsayin koli wajen fitar da hayaki carbon da daidata shi da abubuwan dake iya zuke shi. (Fa’iza Mustapha)