logo

HAUSA

Ministan wajen Iran: Kila Iran za ta daina tattaunawa kan yarjejeniyar nukiliyarta

2022-12-29 10:16:15 CMG Hausa

Ministan harkokin wajen kasar Iran Hossein Amir-Abdollahian ya bayyana cewa, ba zai yiyu kasarsa ta ci gaba da bude tagar sake tattauna batun daddale yarjejeniyar nukiliyarta ba har abada, don haka take bukatar kasar Amurka da sauran sassan da abin ya shafa da su dauki matakan da suka dace a kan lokaci.

Rahotonnin da gidan talibijin na Iran ya gabatar sun nuna cewa, Amir-Abdollahian ya yi tsokacin ne jiya, yayin da yake amsa tambayar manema labarai a kasar Oman, inda ya bayyana cewa, duk da cewa Iran ba ta rufe tagar sake daddale yarjejeniyar a halin yanzu ba, amma idan kasashen yamma suka ci gaba da daukar matakan tsoma baki da ba su dace ba, to Iran za ta rufe tagar.

Amir-Abdollahian, ya kuma tabo batun tattaunawar da aka yi tsakaninsa da babban wakilin kungiyar tarayyar Turai (EU) kan harkokin diplomasiya da manufofin tsaro Josep Borrell a kwanan baya, inda ya bayyana cewa, sassan biyu sun yi musayar ra’ayoyi kuma sun cimma matsaya daya kan wasu batutuwa.

Ya kara da cewa, kasar Oman ta kasance mai shiga tsakani, tsakanin Iran da kasashen yamma cikin dogon lokaci, shi ya sa Iran take fatan Oman za ta gabatar da shawarwarinta domin daddale wata yarjejeniya kan batun nukiliyar, mai ma’ana da karfi da kuma dorewa. (Jamila)