logo

HAUSA

Sin da Malawi sun taya juna murnar cika shekaru 15 da kulla huldar diflomasiyya a tsakaninsu

2022-12-28 16:20:04 CMG Hausa

Ministan harkokin wajen Sin, Wang Yi da takwararsa ta kasar Malawi, Nancy Tembo sun yi musayar sakon taya juna murnar cika shekaru 15 da kulla huldar diflomasiyya tsakanin kasashen biyu.

Cikin sakonsa, Wang Yi ya ce a watan Disamban 2007, Sin da Malawi suka kulla huldar diflomasiyya a hukumance, wanda ya bude sabon babin dangantaka a tsakaninsu. Kuma cikin shekaru 15 da suka gabata, dangantaka a tsakaninsu ta yi saurin kyautatuwa, aminci a tsakaninsu ya yi ta zurfafa, haka kuma, sun yi ta fadada dangantaka a fannoni da dama, kana musaya tsakanin al’ummominsu ya kara zurfi.

Ya ce yayin da aka shiga wani sabon mataki a dangantakarsu, a shirye yake ya hada hannu da Nancy Tembo wajen aiwatar da muhimmiyar matsayar da shugabannin kasashen biyu suka cimma, da goyon bayan juna, da hada hannu wajen kare tsarin huldar kasa da kasa da tabbatar da adalci da daidaito a duniya da kuma inganta dangantakar abota dake tsakanin kasashen biyu, domin ci gaba da samun sabbin sakamako karkashin shawarar Ziri Daya da Hanya Daya da kuma dandalin tattauna hadin gwiwar Sin da Afrika.

A cikin nata sakon, Nancy Tembo ta ce, tun bayan da Malawi ta kulla huldar diflomasiyya da Sin, ake jinjinawa dangantakar abota da moriyar juna dake tsakaninsu. Ta ce gwamnatin Malawi na mika godiyarta ga Sin bisa taimakon tattalin arziki da kwararru a fannoni da dama, da kuma taimakonta wajen bunkasa kwarewar jami’ai da tallafin jin kai. A cewarta, Malawi ta kuduri niyyar daga dangantakarsu zuwa sabon matsayi da fadada damarmakin hadin gwiwa a fannoni daban-daban. (Fa’iza Mustapha)