logo

HAUSA

Babbar Magana

2022-12-28 17:54:36 CMG Hausa

Fari, da ambaliyar ruwa, kwararar hamada, yanayi na sanyi da zafi da suka wuce kima da makamantansu, na daga cikin matsalolin da sauyin yanayi ke haddasawa, wadanda kuma ke ci gaba da addabar bil-adama. Bayanai na nuna cewa, kasashen dake yankin kahon Afirka na daga cikin wadanda ke fama da wannan matsala.

Sakamakon matsalar fari da yankin kahon Afirka ke fuskanta, ya sa asusun tallafawa kananan yara na MDD ko UNICEF a takaice, ya kaddamar da asusun gaggawa, inda yake neman taimakon dalar Amurka biliyan daya, domin tallafawa yaran dake rayuwa a sassan yankin kahon Afirka a shekarar 2023 dake tafe.

UNICEF ya ce, ya sake nazartar kudaden tallafin gaggawa na jin kai da ake bukata, domin kare rayuwar yara dake kasashen Habasha, da Kenya da Somaliya, inda adadin kudaden da ake bukata domin gudanar da ayyuka ya sauya, daga dala miliyan 879 a watan Satumba zuwa dala biliyan daya a shekara mai zuwa. Babbar magana wai Dan-sanda ya ga gawar soja.

Wannan na zuwa ne, bayan asusun da aka kaddamar a taron sauyin yanayi na kasar Masar, duk da nufin magance illar da wannan matsala ta sauyin yanayi ke haifarwa duniyar bil-Adama da abubuwan dake rayuwa a cikinta.

Bayanai na nuna cewa, yaran dake yankin kahon Afirka na fuskantar mawuyacin hali na rayuwa, sakamakon mummunan fari da aka jima ba a ga irin sa ba a tarihin kasashen 3, baya ga tashe-tashen hankula dake ci gaba da addabar arewacin Habasha. Don haka, taimakawa wannan rukuni na al’umma dake zama manyan gobe, zai taimaka ga ci gaban al’ummar yankin ne baki daya.

Masharhanta na cewa, mummunan tasirin sauyin yanayi na barazana ga rayukan yara, abin da ya sanya asusun mayar da hankali, ga dabarun jurewa da iya rayuwa tare da tasirin sauyin yanayi, a matsayin muhimman bangarorin tallafin jin kai da yake aiwatarwa. Kuma hakan zai taimaka matuka, wajen kaiwa ga yaran dake rayuwa cikin yanayin tashe-tashen hankula, tare da ba da damar taimaka musu, da al’ummun su shiryawa abubuwan daka iya aukuwa a nan gaba. Rigakafi aka ce ya fi magani. Fata dai shi ne, kudaden da za a tara za su kai ga wadanda aka yi dominsu. Domin ka da a fake da guzuma ana harbin karsana. (Ibrahim Yaya)