logo

HAUSA

Muhallin halittu ya yi matukar ingantuwa cikin shekaru 10 da suka gabata a kasar Sin

2022-12-28 12:27:03 CMG Hausa

Cibiyar nazarin harkokin kimiyya ta kasar Sin (CAS), ta fitar da jerin rahotannin da suka bayyana cewa, kasar Sin ta samu manyan nasarori a muhallinta na halittu cikin shekaru 10 da suka gabata.

Rahotannin sun nuna cewa, jimilar adadin albarkatun ruwa a tabkunan kasar Sin ta karu sosai. Kuma yanayin hasken ruwan tabkunan na ci gaba da ingantuwa, haka ma mabanbantan halittu a wasu muhimman tabkuna.

Har ila yau, rahotannin sun ruwaito cewa, baki dayan yankuna masu danshi na ci gaba da farfadowa yayin da ake samu nasara a fannin kare halittun dake wuraren.

A bangaren tsaunika kuwa, aikin kariya da takaita zaizayar kasa na tafiya yadda ya kamata, kuma an kafa wani ingantaccen tsarin kandagarki da takaita aukuwar annoba.

Bugu da kari, rahotannin sun ce tsimin ruwa a yankuna masu karancin ruwa dake arewa maso yammacin kasar Sin ya samu kyakkyawan sakamako, inda aka samu karuwar ingancin amfani da ruwa da kuma fadada yankunan amfani da tsarin ban ruwa dake tsimin ruwan. (Fa’iza Mustapha)