logo

HAUSA

Iran: Har yanzu kofar Iran a bude take domin farfado da yarjejeniyar nukiliyarta

2022-12-27 10:47:11 CMG Hausa

Ma’aikatar harkokin wajen Iran ta ce, har yanzu kofar kasar ta tattaunawa a bude take, domin farfado da yarjejeniyar nukiliyar kasar ta 2015.

Kamfanin dillancin labarai na kasar IRNA ya ruwaito kakakin ma’aikatar, Nasser Kanani na bayyanawa jiya, yayin taron manema labarai na mako-mako cewa, za a iya cimma yarjejeniya idan bangaren yammacin duniya ya nuna aniyar hakan.

A cewarsa, an samar da kyawawan damarmaki domin farfado da yarjejeniyar da cire takunkuman da aka sanyawa kasar yayin tattaunawar da aka yi a baya, tsakanin Iran da mai shiga tsakani na tarayyar Turai da kuma wanda aka yi a gefen taron hadin gwiwa na Baghdad da aka yi makon da ya gabata a Amman na Jordan.

Ya ce Washington ta rasa damarta ta cimma matsaya dangane da yarjejeniyar, bayan ta fake da zaben tsakiyar wa’adi na kasar da aka yi a watan Nuwamba, a lokacin da ake shirin sanya hannu kan yarjejeniyar. (Fa’iza Mustapha)