logo

HAUSA

Mabiya addinin Krista a Najeriya sun yi addu’o’in samun shugabannin da za su kawo karshen kashe-kashe da yawan garkuwa da jama’a a kasa

2022-12-26 15:06:39 CRI

A ranar 25 ga wata ne mabiya addinin Krista a tarayyar Najeriya suka bi sahun sauran takwarorinsu na duniya wajen gudanar da shagul-gulan bikin Kirsimeti na wanann shekara.

A yayin bukukuwan shugabannin mujami’o’i daban daban sun jagoranci addu’o’in samun zaman lafiya a kasar da kuma kira ga mibiya da su kasance masu kaunar kasa tare da mutunta junan su.

Daga tarayyar Najeriya wakilinmu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto.

Bikin Kirsimetin na bana ya banbanta da na sauran shekaru bisa la’akari da yanayin tsaro da tsadar rayuwa.

Ha’ila yau ba kamar yadda aka saba ba, al’adar ziyartar juna a irin wannan lokaci na Kirsimeti ya yi karanci a bikin na bana saboda rashin  tabbas na tsaro a kan tituna yayin da kuma sufuri ta jiragen sama ya yi tsada matuka.

Akasari dai a bana shugabanni da malaman coci-coci sun mayar da hankali wajen amfani da kafofin yada labarai domin yada fatan alherinsu ga mabiya tare kuma da yin kira a gare da su koma ga Allah wajen neman tabbatacciyar makoma ga kasa.

A sakonsa na Kirsimeti, shugaban kungiyar Kiristoci reshen jihar Kaduna dake arewacin Najeriya Rev Josep Hayaf ya tabo kadan daga cikin kyawawan halayen annabi isa ASW wanda ya yi koyi da kaunar juna da yafiya.

“Rayuwar Yesu Kristi ya kunshi abubuwa da dama cikin rayuwa, na farko biyayya ga shugabanni, na biyu yi wa kasa addu’a da bin doka, na uku kauna da Allah ya yi wa duniya da kuma samun alfarmar Allah ba domin ka cancanta ba, wannan shi ne abin da muke kara tunatar da mabiya a wannan lokaci na kirsimeti.”

Shugaban kungiyar kiristocin reshen jihar Kaduna dake arewacin Najeriya ya shawarci mabiya addinin na Kirista a duk inda suke a Najeriya da su himmatu wajen yin addu’a ga kasa.

A kan masu son yin tafiye-tafiye kuwa domin gudanar da shagulgulan bikin Kirsimetin a wasu garuruwa, Rev Josph Hayaf ya ba su shawara kamar haka.

“Sabo da har yanzu sha’anin tsaro bai gyaru ba, ana kan satar mutane ana ci gaba kuma da kashe mutane a wasu wuraren, wanann na tsorata mutane ba za su iya tafiya ba, a nan muna kira ga jama’a cewa, ba sai lallai ka yi tafiya za ka yi Kirsimeti ba, kana iya zauna a ko’ina ka yi Kirsimetin ka, ka yi addu’o’inka duk inda kake Allah yana tare da kai.”

Tun dai a makon jiya ne gwamnatin tarayya ta kebe 26 da 27 ga wannan wata na Disamba da kuma 2 ga watan gobe na Janairu a matsayin ranakun hutun Kirsimeti da na sabuwar shekara domin baiwa ma’aikata da sauran al’ummar kasa damar gudanar da bukukuwa cikin natsuwa. (Garba Abdullahi Bagwai)