logo

HAUSA

Sojojin Najeriya sun kashe mayakan Boko Haram fiye da 100 a yankin arewa maso gabashin kasar

2022-12-26 19:26:55 CMG HAUSA

 

Mai magana da yawun rundunar sojojin saman Najeriya Edward Gabkwet, ya bayyana cewa, sojojin saman kasar, sun yi nasarar kashe mayakan Boko Haram sama da 100, a wani samame da suka kai a jihar Borno da ke yankin arewa maso gabashin kasar.

Kakakin ya bayyana a cikin wata sanarwa cewa, an kai samamen ne a makon da ya gabata, bayan wani rahoton sirri dake nuna cewa, wani kwamandan Boko Haram ya koma wani kauye a jihar Borno da manyan motocinsa, sannan kuma wasu ‘yan ta’adda masu tsattsauran ra’ayi daga wasu wurare sun hade da su.

Gabkwet ya bayyana cewa, an kashe 'yan ta'adda da dama a hari na farko da sojojin saman suka kai, sannan an kashe wasu da dama a hare-haren da suka biyo baya, yayin da wasu mayakan da suka tsira suka dawo domin kwashe gawarwakin wadanda aka kashe.

A cewarsa, wannan farmakin ya rage wa 'yan Boko Haram din karfinsu na sake haduwa da ma kai wa 'yan kasa hari a lokacin bukukuwan kirsimeti da sabuwar shekara da kuma babban zabe dake tafe, (Ibrahim)