logo

HAUSA

Falasdinawa sun yi zanga-zangar neman a ba su gawawwakin ’yan uwan su da Isra’ila ta rike

2022-12-26 11:37:47 CMG Hausa

Gwamman Falasdinawa sun gudanar da zanga-zanga, da nufin neman tsagin Isra’ila ya mayar musu da gawawwakin ’yan uwan su da sojojin Isra’ilan suka rike tsawon shekaru.

Rahotanni sun ce masu zanga-zangar ta jiya Lahadi, sun rika daga tutoci da hotunan wadanda sojojin Isra’ila suka hallaka, lokacin da suke kokarin kaiwa yankunan Isra’ila hari.

Masu zanga-zangar karkashin jagorancin kungiya mai rajin kare hakkin Falasdinawa, sun keyawa titunan birnin Ramallah na yamma da kogin Jordan, suna furta kalaman dake bayyana bukatar karbar gawawwakin ’yan uwan su da yaransu.

Wata sanarwa da iyalan wadanda aka rike gawawwakin nasu suka fitar, ta yi kira ga kungiyoyin kare hakkin bil adama na sassan kasa da kasa, da su yiwa mahukuntan Isra’ila matsin lamba, domin ta mika musu gawawwakin.

Sanarwar ta ce mahukuntan Isra’ila, sun ajiye gawawwakin Falasdinawan ne cikin wasu dakunan sanyaya gawawwaki, da wasu kaburbura da aka yiwa alamu. Kaza lika sanarwar ta ce ’yan uwan mamatan za su ci gaba da bore har sai an mika musu gawawwakin.

Gwamnatin Isra’ila dai na rike da sama da gawawwakin Falasdinawa 100, wadanda ta zarga da yunkurin kaiwa yankunan ta hari tun daga shekarar 2015, ta kuma ki amincewa ta mika su ga iyalan su.  (Saminu Alhassan)