logo

HAUSA

Kasar Saliyo ta yi wani kokari na dakile safarar miyagun kwayoyi

2022-12-25 15:05:21 CMG HAUSA

 

Kasar Saliyo ta lalata haramtattun kwayoyi masu tarin yawa, a wani kokari na yaki da matsalar safarar miyagun kwayoyi a kasar dake yammacin Afirka.

Rundunar 'yan sandan kasar Saliyo tare da hadin gwiwar hukumomi da jami'an tsaro sun lalata magungunan a bainar jama'a.

Sashen watsa labarai na rundunar 'yan sandan kasar, ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewa, magungunan da aka lalata, sun hada da kilogiram 135 na tabar wiwi, da kuma kwalaye sama da dubu 2 naTramadol, inda suka bayyana cewa, manufar matakin ita ce, dakile masu shigo da kayayyakin da kuma dillalan wadannan magunguna da abubuwa masu hadari cikin kasar.

Jami’an kwastam da na tashar jiragen ruwa sun bayyana cewa, an kama mafi yawan kwayoyin Tramadol ne a tashar ruwan Saliyo.

Wani likita a Saliyo mai suna Ibrahim Sesay, ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewa, an shigo da wasu daga cikin Tramadol ne domin a yi amfani da su ba bisa ka'ida ba, kamar sayarwa matasa domin amfani da su ta hanyar da ba ta dace ba.(Ibrahim)