logo

HAUSA

Rundunar sojin Najeriya ta lalata haramtattun matatun mai guda 57 sannan ta kama barayin mai 21

2022-12-24 15:30:48 CRI

A ranar 22 ga wata yayin wani taron manema labarai, hedikwatar tsaron Najeriya ta tabbatar da cewa ta samu gagarumin nasara a yakin da take yi da ’yan ta’addan yankin Niger Delta wanda ya kunshi jahohin Bayelsa, Delta da Rivers.

Kamar yadda daraktan harkokin yada labaran hedikwatar tsaron Major General Musa Dan-madami ya bayyana cewa, dakarun rundunar sun yi kokarin dakile yunkurin fasa bututun mai da dama .

Daga tarayyar Najeriya wakilinmu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da ci gaban rahoton.