logo

HAUSA

Jakadan Sin a Nijar ya gana da uwargidan shugaban kasa

2022-12-24 15:14:00 CMG Hausa

Jakadan kasar Sin a janhuriyar Nijar Jiang Feng, ya zanta da uwargidan shugaban kasa, kuma shugabar gidauniyar Noor malama Hadiza Bazoum.

Yayin tattaunawar ta su a ranar Alhamis, jakada Jiang ya mika wasikar gaisuwa ta uwargidan shugaban kasar Sin farfesa Peng Liyuan, ga uwargida Hadiza Bazoum, yana mai cewa, farfesa Peng Liyuan na dora muhimmancin gaske ga harkokin da suka shafi mata da yara kanana dake nahiyar Afirka, tana kuma jinjinawa madam Hadiza, da gidauniyar ta ta Noor, bisa kwazon su na yayata bukatar daga matsayin mata, da kyautata rayuwar rukunonin al’umma masu rauni dake Nijar.

Kaza lika Jakada Jiang, ya sha alwashin kara azamar karfafa tattaunawa da hadin gwiwa da gidauniyar Noor, da ma ba da karin gudummawar kyautata rayuwar al’ummar Nijar.

A nata tsokaci kuwa, uwargida Hadiza Bazoum, godewa farfesa Peng Liyuan ta yi, bisa wasikar da ta aike mata, tana mai jinjinawa gudummawar Peng a fannin bunkasa rayuwar mata da yaran Afirka, ciki har da na janhuriyar Nijar.

Kaza lika ta godewa jakada Jiang, bisa gudummawar da ofishin sa ya jima yana baiwa gidauniyar ta, ta kuma sha alwashin aiki tare da ofishin jakadancin Sin dake Nijar, ta fannin zurfafa abota tsakanin al’ummun kasashen 2, da ingiza ci gaban dangantakar su.  (Saminu Alhassan)