logo

HAUSA

Hukumar NBC ta Najeriya na daukar matakan samar da dokokin sanya ido kan kafofin labarai na kafar intanet

2022-12-23 10:13:53 CMG Hausa

A ranar 21 ga wata ne yayin wani taron masu ruwa da tsaki kan harkokin zabe a Najeriya, hukumar lura da kafofin yada labarai NBC ta ce tana kokarin ganin an samar da dokokin da za su ba ta karfin ikon hukunta kafofin labarai dake shafin yanar gizo wadanda suke aiki kara zabe.

Shugaban hukumar Balarabe Shehu Illela ne ya tabbatar da hakan yayin wani taron masu ruwa da tsaki kan harkokin zabe 2023 a birnin Abuja, hedikwatar mulkin tarayyar Najeriya.

Daga tarayyar Najeriyar wakilin mu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da cigaban labarin.

 

Taron dai ya gudana ne a lokacin da ya rage kasa da kwanaki 60 a gudanar da babban zaben a tarayyar Najeriya.

Malam Balarabe Shehu Illela ya ce karuwar kafofin labarai da suke amfani da yanar gizo a Najeriya wani lokaci yana barazana ga yanayin tsaro da zaman lafiyar kasar.

Ya ce akasarin masu wadannan kafofin labarai ba sa nuna kwarewar da ta kamata, sannan kuma wasun su ’yan siyasa na amfani da su wajen yada labaran son zuciya.

“Kowane abu ana yi ne bisa tsarin doka, akwai dokar da ta tanadi cewa mu kula da kafafen yada labarai da aka saba amfani da su wato Rediyo da Talabijin. A lokacin da aka kafa hukumar NBC babu wadannan kafofin labaran da suke yanar gizo saboda haka ba ka da ikon hukunta irin wadannan kafofi tun da ba ka tanadi doka a kan su ba, amma yanzu muna daukar matakai na ganin cewa mun samu dokoki da za su ba mu dama wajen hukunta kafofin labarai dake yanar gizo wajen aikata wadannan laifufuka din.”

Da yake nasa jawabin yayin taron, shugaban hukumar zabe mai zaman kanta ta tarayyar Najeriya Farfessa Mahmud Yakubu ya ce duk da kalubalen tsaro a wasu sassan Najeriya, amma hukumar tana da karfi gwiwar gudanar da sahihin zabe da ba`a taba yin irinsa ba a kasar, har kuwa da jahohin da aka samu rahotannin wasu ’yan ta’adda sun kone ofisoshin hukumar.

“Dukkanmu baki ya zo daya a kan cewa za mu dauki mataki don magance amfani da kudi wajen gurbata harkar zabe a Najeriya musamman sayen kuri’u da wasu suke yi ranar zabe, wannan bai kamata ba. Kididdigar da muka yi ya zuwa watan jiya na Nuwanba ya nuna cewa akwai tashin hankali da aka samu har sau 52 a jahohi 19 a fadin Najeriya, kuma abin mamaki shi ne, wadannan abubuwa sun faru ne a cikin watanni 2 da fara yaki neman zabe. Shi ya sa muke ganawa da jami’an tsaro da sauran masu ruwa da tsaki don mu sami yadda za mu shawo kan wannan matsala.”

Taron dai ya samu wakilcin kungiyoyin fararen hula, jami’an tsaro, wakilan ofisoshin jakadanci kasashen waje da ’yan jaridu na gida da na kasashen ketare. (Garba Abdullahi Bagwai)