logo

HAUSA

Amurka ta sanar da bada karin tallafin soji na dala biliyan 1.85 ga Ukraine

2022-12-22 11:28:59 CMG Hausa

Shugaban Amurka Joe Biden, ya ce Amurka za ta samar da karin tallafin soji na dala biliyan 1.85 ga Ukraine, ciki har da na’urorin kakkabo makamai masu linzami.

Sanarwar na zuwa ne yayin da shugaban Ukraine Volodymyr Zelenskyy ya isa Washington, ziyara ta farko da ya kai wata kasa tun bayan fara rikicin kasarsa da Rasha, kimanin kwanaki 300 da suka gabata.

Shugaba Biden ya yi wa Shugaba Zelenskyy maraba da zuwa fadar White House, domin tattauna dangantakar kasashen biyu, yana mai alkawarin Amurka za ta ci gaba da karfafa karfin Ukraine na kare kanta, musamman ta sama.

A nasa bangare, shugaba Zelenskyy ya ce alkawarin Amurka na samar da na’urorin kakkabo makamai masu linzami, muhimmin mataki ne na samun ingantacciyar kariya ta sama.

Cikin wata sanarwa, sakataren harkokin wajen Amurka Anthony Blinken, ya ce tallafin ya hada da dala biliyan 1 a bangaren fadada kariya ta sama da karfin kai hare-hare daidai inda aka auna, da kuma dala miliyan 850 na tallafin tsaro. (Fa’iza)