logo

HAUSA

MDD ta kaddamar da shirin agajin jin kai ga Sudan ta Kudu a 2023

2022-12-21 11:21:10 CMG HAUSA

 

An kaddamar da wani shirin agajin jin kai da darajarsa ta kai dala biliyan 1.7, domin taimakawa mutane miliyan 6.8 mafiya rauni a kasar Sudan ta Kudu. 

Kakakin MDD Stephane Dujarric, ya bayyana cewa, shirin wanda aka kaddamar a jiya Talata, wanda kuma zai fara aiki a shekarar 2023, na da nufin taimakawa mutanen da rikici ya rutsa da su da wadanda ke fama da mummunan tasirin yanayi da masu gudun hijira. 

Stephane Dujarric ya ruwaito babbar jami’ar dake kula da ayyukan agajin jin kai a Sudan ta Kudu Sara Nyanti na cewa, yayin da Sudan ta Kudu ke fama da tarin matsaloli da rashin kudi, al’ummar kasar na bukatar karin tallafi domin su samu damar rayuwa.

Ta kuma jaddada bukatar ba ma’aikatan agaji damar isa ga mutane mabukata ba tare da wani cikas ba. 

A cewar Stephane Dujarric, sama da kaso 2 cikin 3 na al’ummar Sudan ta Kudu na bukatar wani tsarin agajin jin kai da kariya a shekarar 2023. (Fa’iza Mustapha)