logo

HAUSA

Kwamitin tsaron MDD ya tsawaita wa’adin tawagar wanzar da zaman lafiya ta MDD dake Congo (Kinsasha) da shekara daya

2022-12-21 14:09:01 CMG Hausa

Kwamitin tsaron MDD ya zartar da kuduri mai lamban 2666 a jiya Talata, wanda ya tsawaita wa’adin tawagar wanzar da zaman lafiya ta MDD dake Congo (Kinsasha) da shekara daya, zuwa ranar 20 ga watan Disamba na shekarar 2023.

Bisa kudurin, aikin farko na tawagar wanzar da zaman lafiya ta MDD dake Congo (Kinsasha) shi ne kare fararen hula da daidaitawa da karfafa hukumomin kasar Congo (Kinsasha), da kuma goyon bayan tsarin mulkin kasar da gyare-gyare a fannin tsaro.

Kudurin ya ce, jami’an tawagar wanzar da zaman lafiya ta MDD dake Congo (Kinsasha), sun hada da jami’an sojoji dubu 13.5, cikinsu akwai sojoji masu sa ido da ma'aikata 660, sai ’yan sanda 591 da wasu ’yan sandan musamman 1410. Kudurin na bukatar sakatariyar MDD ta yi la'akari da rage tura sojojin tawagar wanzar da zaman lafiya zuwa Congo (Kinsasha).  (Safiyah Ma)