logo

HAUSA

António Guterres:Dole ne a warware rikicin Rasha da Ukraine cikin lumana bisa Tsarin Dokokin MDD

2022-12-20 11:23:36 CMG Hausa

Babban sakataren MDD António Guterres ya gudanar da taron manema labarai a jiya Litinin, inda ya tattauna da ’yan jarida game da wasu batutuwan kasa da kasa kamar rikicin Rasha da Ukraine.

Guterres ya bayyana cewa, ba shi kwarin gwiwar tattaunawar zaman lafiya tsakanin Rasha da Ukraine nan gaba kadan. Ya kuma jadadda cewa, dole ne a warware rikicin Rasha da Ukraine cikin lumana bisa Tsarin Dokokin Majalisar Dinkin Duniya. Ya ce, MDD za ta ci gaba da samar da dandalin tattaunawa, don rage hasarar rayuka. Don haka, yana fatan bangarorin Rasha da Ukraine za su gaggauta kawo karshen rikicin, da warware matsalar rashin jituwa da ake fama da ita ta hanyar tattaunawa.

Guterres ya bayyana cewa, ana ci gaba da aiwatar da yarjejeniyar fitar da hatsi ta tekun Bahar Maliya, kuma MDD za ta ci gaba da aiwatar da yarjejeniyar da aka cimma tare da Rasha, wajen tallafawa Rasha fitar da hatsi da takin zamani.

Guterres ya kara da cewa, MDD tana fatan ci gaba da fadada yarjejeniyar fitar da hatsi ta tekun Black Sea, da kara fitar da hatsi zuwa kasashen waje, da fadada yawan tashoshin jiragen ruwan Ukraine da aka ba su izinin fitar da su zuwa kasashen waje. (Safiyah Ma)