logo

HAUSA

Jimillar Jarin Da Asusun Raya Kasashen Sin Da Afirka Ya Zuba Ta Zarce Dalar Amurka Biliyan 5

2022-12-20 11:04:38 CMG HAUSA

Asusun raya kasar Sin da kasashen Afirka, asusun da bankin raya kasar Sin ke gudanarwa, ya sanar da cewa, ya zuwa yanzu ya zuba jarin sama da dalar Amurka biliyan 5 a kasashen Afirka,

Bangarorin da asusun ya zuba jarin sun hada da ababen more rayuwa, da aikin noma, da rayuwar jama'a, da inganta hadin kai a masana’antu, da wuraren raya masana'antu, da sauran fannoni, kuma jarin ya taimaka wajen habaka tattalin arzikin kasashen Afirka, da samar da ayyukan yi, da kudaden shiga na haraji a Afirka.

Asusun ya dimbin jarin a fannoni da dama a Afirka, lamarin da ya zama abun misali wajen kara azama kan aiwatar da shawarar “ziri daya da hanya daya” cikin hadin gwiwar kasar Sin da kasashen Afirka.

An kafa asusun ne a shekarar 2007, bayan kammala taron kolin na dandalin tattaunawar hadin gwiwa tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka (FOCAC) na shekarar 2006 a birnin Beijing domin tallafa wa kamfanonin kasar Sin dake nahiyar Afirka, inda ya fara da jarin dalar Amurka biliyan 5 a karon farko.

Ya zuwa yanzu, asusun ya yanke shawarar zuba jarin sama da dalar Amurka biliyan 6.6 a wasu ayyuka a kasashen Afirka 39, ya kuma jawo jarin sama da dalar Amurka biliyan 31 daga kamfanonin kasar Sin.(Ibrahim)