logo

HAUSA

Sojojin Somaliya sun kashe mayakan al-Shabab 150

2022-12-20 11:09:27 CMG HAUSA

 

Rundunar sojan kasar Somaliya ta sanar da cewa, dakarunta sun yi nasarar kashe 'yan ta'addar Al-Shabab 150, a wani samame na tsawon mako guda da suka kaddamar a yankin Shabel ta tsakiya dake kasar.

Babban hafsan hafsoshin tsaron kasar Odowaa Yusuf Rage ya ce an kashe mayakan na Al-Shabab da dama, a kusa da garin Aden Yabal, wanda ke zama tungar kungiyar a baya, amma aka kwato shi a baya-bayan nan.

Hare-haren na baya-bayan nan sun zo ne, a daidai lokacin da dakarun gwamnati suka samu nasara, inda suka 'yantar da yankuna da dama a tsakiyar kasar Somaliya a ‘yan kwanakin nan. (ibrahim).