logo

HAUSA

Binciken jin ra'ayin jama'a ya nuna yawancin masu jefa kuri'a ba su da kwarin gwiwa game da makomar tattalin arzikin Amurka

2022-12-19 12:01:23 CMG Hausa

Sakamakon wani kuri’ar jin ra’ayin jama’a da jaridar The Wall Street Journal dake Amurka ta fitar a kwanan nan ya nuna cewa, yawancin masu jefa kuri'a, ba su da kwarin gwiwa game da makomar tattalin arzikin Amurka a shekarar 2023, kuma kusan kashi biyu bisa uku daga cikinsu suna tsammanin cewa, tattalin arzikin Amurka yana kan hanyar da ba ta dace ba.

Jaridar Wall Street Journal ta gudanar da bincike kan masu jefa kuri'a 1,500 daga na ran 3 zuwa 7 ga wata, Sakamakon binciken ya nuna cewa,  galibin masu jefa kuri'a suna ganin tattalin arzikin Amurka zai ci gaba da tabarbarewa, kuma kashi 83 cikin 100 na masu jefa kuri'a ’yan Republican suna ganin tattalin arzikin Amurka zai yi muni a shekarar 2023. A sa’i daya kuma, kashi 66% na masu jefa kuri’a suna tsammanin tattalin arzikin Amurka yana kan hanyar da ba ta dace ba.

Tun farkon wannan shekara, hauhawar farashin kayayyaki ya ci gaba da addabar tattalin arzikin Amurka. Don hana hauhawar farashin kayayyaki, babban bankin tarayyar Amurka, ya kara kudin ruwa sau bakwai a jere tun daga watan Maris, inda ya kara 4.25%, kuma yana tsammanin kamata ya yi a ci gaba da kara kudin ruwa a nan gaba. Ko da yake a cikin watanni biyu da suka gabata, saurin karuwar CPI na Amurka ya samu sassauci bisa makamancin lokaci na bara, amma har yanzu ya karu fiye da 2%, wato ya karu fiye da kima. A sakamakon tasirin hauhawar kayayyaki da karuwar kudin ruwa, ana ci gaba da nuna damuwa cewa, tattalin arzikin Amurka zai ci gaba da tabarbarewa a kullum. (Safiyah Ma)