logo

HAUSA

Argentina ta doke Faransa a bugun daga kai sai mai tsaron gida inda ta lashe kofin duniya

2022-12-19 10:34:05 CMG Hausa

Argentina ta doke Faransa a bugun fenariti, inda ta lashe gasar cin kofin duniya ta FIFA ta 2022 da aka kammala a Qatar. Saura mintuna uku a kammala wasan ne, Faransa ta samu bugun daga kai sai mai tsaron gida, bayan da dan wasan Argentina Gonzalo Montiel ya taba kwallon a cikin da’irar mai tsaron gida.

Dan wasan Faransa, Klian Mbappe ya sake zura kwallon, abin da ya ba shi damar zura kwallaye uku rus a wasan, hakan ya sanya shi zama dan wasan da ya fi kowa zura kwallaye a gasar cin kofin duniyar ta bana.

Kungiyoyin biyu dai sun samu karin damar lashe wasan, amma babu wanda ya iya zura kwallo a raga, hakan ya sa wasan ya kai ga bugun daga kai sai mai tsaron gida. Daga nan ne Argentina ta samu nasara, bayan da ’yan wasan Faransa guda biyu, Kingsley Coman da Aurelien Tchouameni suka barar da bugun daga kai sai mai tsaron gida. (Ibrahim Yaya)