logo

HAUSA

An amince da kudurin aiki na Kunming-Montreal game da kare mabambantan halittu yayin taron COP15

2022-12-19 20:16:05 CMG Hausa

A Litinin din nan ne aka amince da kudurin aiki na MDD, game da shawo kan koma baya da aka samu, da asarar da aka tafka a fannin kare mabambantan halittu, tare da dora duniya kan turbar farfadowa daga wadannan matsaloli.

An amince da kudurin ne yayin taro zagaye na biyu, na wakilan bangarorin da suka sanya hannu kan jarjejeniyar kasancewar mabambantan halittu karo na 15 ko COP15.

Kudurin mai taken “Tsarin aikin Kunming da Montreal game da kare mabambantan halittu”, ya samu amincewa daga manyan masu ruwa da tsaki, wadanda suka yi na’am da manufofin sa, da burikan da yake kunshe da su, da samar da albarkatun gudanarwa da na bayanai ko “GSI”, wadanda ake bukata domin cimma nasarar kudurin.

Kasar Sin ce ke rike da shugabancin taron na COP15. Kuma ita ce ta jagoranci zagayen farko na taron a birnin Kunming, fadar mulkin lardin Yunnan dake kudu maso yammacin kasar a shekara 2021 da ta gabata. Yayin da birnin Montreal na kasar Kanada, ya dora daga inda aka tsaya a zagaye na biyu na taron, bisa taken "Wayewar kai game da muhallin halittu: Gina makomar bai daya ga daukacin rayukan dake doron duniya." (Saminu Alhassan)