logo

HAUSA

Shugaban kwalejojin fasaha mallakin gwamnatin jihar Gombe ya bukaci da a yi koyi da kasar Sin wajen mayar da wasu jami`o’i zuwa kwalejojin fasaha a Najeriya

2022-12-18 14:55:13 CMG Hausa

Yayin da takaddama tsakanin gwamnatin tarayyar Najeriya da malaman jami`o’i ta ki karewa, an yi kira da a soke mafi yawan jami`o’in da ake da su ta hanyar mayar da su zuwa kwalejojin fasaha domin hakan ita ce mafita da za ta baiwa matasa damar koyon sana`o’in hannu.

Shugaban rukunin kwalejojin fasaha mallakin gwamnatin jihar Gombe Dr. Abbas Umar Faruk ne ya bukaci hakan ga manema labarai a garin Gombe dake arewa maso gabashin Najeriya.

Dr Abbas Umar Faruk ya ce akwai bukatar rage jami’o’in da ake da su a Najeriya, a maida su makarantun kimiya da fasaha, a cewarsa haka ne kadai hanyar da za ta baiwa matasa damar dogaro da kansu bayan sun kamala karatun gaba da sakandare maimakon dogaro da gwamnati wajen samun aiki.

“A China yanzu sun mayar da wasu jami`o’insu zuwa kwalejojin fasaha ganin mahimmancin irin wadannan kwalejoji ya zartar na jami`o’in sosai, duk da cewa su ma jami`o’in akwai wadanda tsarin darussansu ya danganci fasaha.

Ka ga yanzu kasar China na daya daga cikin kasashen da suka ci gaba a duniya amma duk da haka suka dauki matakin juya wasu jami`o’insu zuwa kwalejojin fasaha.

Sabo da haka ina ganin mu ma a nan Najeiya mu yi amfani da irin wanann dama wajen koyi da kasar Sin, idan ka duba a nan ba kowanne yaro ne yake da karfin kwakwalwar da zai iya fahimtar karatu kai tsaye ba tare da an nuna masa misalai a zahirance ba.”

Haka zalika Dr. Abbas Umar Faruk ya jaddada bukatar a kara samarwa kwalejin kimiya da fasaha dake Gombe karin dakunan kwanan dalibai, domin rashin dakunan yana mutukar shafar kwazon dalibai.

Ya ce kusan sama da rabin dalibai maza na zaune ne a cikin gari maimakon harabar jami’ar, wannan na kashe gwiwar iyayensu rinka turo ’ya’yansu wannan kwaleji domin karatu.

Ko da yake ya ce matsalar tsaro ma na ci masu tuwo a kwarya.

“Wani abu da muka hanga na hana yara zuwa wannan kwaleji shi ne matsalar tsaro, saboda makarantar na da iyaka da jahohin Yobe da Borno.”

Ya zuwa yanzu dai adadin jami`o’i a tarayyar Najeriya sun kai 170, daga cikin wannan adadi kuma 79 na masu zaman kansu, sai 43 mallakin gwamnatin tarayya yayin da 48 kuma mallakin jahohi ne. (Garba Abdullahi Bagwai)