logo

HAUSA

Croatia ta zamo ta uku a gasar cin kofin duniya bayan ta doke Morocco da ci 2-1

2022-12-18 16:17:22 CMG Hausa

Croatia ta doke Morocco da ci 2 da 1, a wasan neman matsayi na 3 da suka buga a jiya Asabar, wanda hakan ya ba ta damar sake lashe wannan matsayi a karo na biyu, bayan da ta kasance ta 3 a gasar cin kofin na hukumar FIFA da aka buga a shekarar 1998, inda a wancan lokacin ta doke Netherlands da ci 2 da 1.

A gasar cin kofin na kwallon kafa na shekarar 2018 kuwa, Croatia ta kasance a mataki na 2 ne, bayan da Faransa ta lashe kofin gasar.

A nata bangare kuwa, Morocco ta kasance kasar Afirka ta farko da ta kai wasan kusa da na karshe, bayan ta rasa nasara a wasannin ta biyu na karshe a gasar. Sai dai duk da haka, za a ci gaba da tunawa da kasar a matsayin wadda ta yi rawar gani a gasar ta kasar Qatar, kasancewar ta wadda ta fito da kimar Afirka da ma kasashen Larabawa a gasar ta bana. (Saminu Alhassan)