logo

HAUSA

Faransa ta kai wasan karshe bayan da ta doke Morocco da ci 2-0

2022-12-15 12:15:07 CMG Hausa

Yayin wasan kusa da na karshe na gasar cin kofin kwallon kafa na duniya da aka buga a jiya Laraba tsakanin kasashen Faransa da Morocco, Faransa ta yi nasara da ci biyu da nema. Wanda hakan ya baiwa Faransar damar kaiwa wasan karshe na gasar, inda za ta fafata da Argentina.

Mintuna 5 da take wasa ne Theo Hernandez ya ci wa Faransa kwallon farko, aka kuma tafi hutun rabin lokaci 1-0. Sai kuma kwallon da  Mbappe ya sakawa Kolo Muani, inda nan take Kolo ya jefa ta a ragar Morocco a minti na 79. A karshe dai an tashi wasan Faransa na da kwallo 2, Morocco kuma na nema.(Safiyah Ma)