logo

HAUSA

Amurka da Sin da Birtaniya da Jamus da Japan kasashe ne dake kan gaba a fannin kimiyyar hallitu da likitanci

2022-12-15 20:15:30 CMG HAUSA

 

Shahararriyar cibiyar wallafe-wallafen ilimi ta kasa da kasa ta Springer Nature ta ba da labari a yau Alhamis cewa, karin mujallar Nature da ta wallafa a wannan mako mai suna “Yanayin ilmin halittu da likitanci na shekarar 2022”, wadda ta bayyana canjin kasashe da yankuna daban-daban a fannin hallitu da likitanci, musamman ma a lokutan barkewar cutar COVID-19, Amurka da Sin da Birtaniya da Jamus da Japan su ne kan gaba a duniya a wannan fanni daga shekarar 2015 zuwa 2021.

Alkaluman da ta fitar na nuna cewa, daga cikin manyan kasashen da ke kan gaba a fannin hallitu da likitanci a duniya, Sin da Birtaniya da Holland da Isra’ila sun kara samun bunkasuwa tun daga shekarar 2019. (Amina Xu)