logo

HAUSA

Sin ta nuna rashin jin dadi kan yadda Birtaniya ta mayar da martani kan abin da ya faru a karamin ofishin jakadancinta dake Manchester

2022-12-15 19:27:02 CMG Hausa

Ofishin jakadancin kasar Sin da ke Biritaniya ya bayyana cewa, sanarwar da Burtaniya ta bayar game da tashe-tashen hankula da suka faru a karamin ofishin jakadancin kasar Sin da ke Manchester, jirkita gaskiya ne kuma bai dace ba.

Ofishin jakadancin ya ce, lamarin da ya faru ne a ranar 16 ga watan Oktoba, abu ne mai tayar da hankali wanda masu adawa da kasar Sin suka shirya da gangan.

Wata sanarwa da ofishin jakadancin kasar Sin dake Burtaniya ya fitar, ta bayyana cewa, mutanen sun kutsa kai ne cikin harabar ofishin ba bisa ka'ida ba, tare da kai farmaki ga jami'an ofishin, wanda hakan ya yi matukar tauye lafiya da martabar jami'an ofishin jakadancin.

Wadanda suka aikata wannan danyen aiki, ba su yi komai ba wajen aiwatar da abin da ake kira 'yancin fadin albarkacin baki, sai dai kawai tayar da hankali. (Ibrahim)