logo

HAUSA

Masana:Matsalar talauci da wasu daga cikin al’adu a Najeriya na daga cikin matsalolin dake taka rawa wajen ta’azara halin cin zarafin mata da yara kanana

2022-12-14 12:32:04 CRI

Binciken masana a tarayyar Najeriya da hukumar kare hakkin bil-adama da asusun lura da kananan yara ta Majalisar Dinkin Duniya ya nuna cewa yara da shekarun su ya kai 15 na fuskantar cin zarafi a Tarayyar Najeriya.

Wannan bincike ya zo daf da lokacin da za` a fara bikin ranar kare hakkin mata da kananan yara a duniya.

A kan haka ne wakilin mu dake Tarayyar Najeriya Garba Abdullahi Bagwai ya shirya mana rahoto na musamman tare da jin ra’ayoyin masana da kwararru a kan kare hakkin bil`adama a Najeriya.

Wadannan alkalluma na zuwa ne dai-dai lokacin da Hukumar kare hakkin bil adama ta fidda  kiddidigar dake nuni da cewa sama da matan aure da kananan yara mata miliyan guda ne aka samu an ci zarafinsu a shekarar 2022.

A cewar rahoton Hukumomin ciki da wajen Najeriyar, Mata kan fuskanci cin zarafi ta hanyar duka ko kuma hana su samun ingantattaciyar rayuwa, inda rahoton Majalisar Dikin Duniyar a hannun guda ya yi nuni dacewa sama da kashi 85 na mata a duniya sun taba fusakantar wani nau’in cin zarafi.

Ga ta bakin Babban Magatakardar Majalisar Dikin Duniya, Antonion Guteres…

“Ina kiran da a kawo karshen tashin hankali a ko ina a duniya, to amma a sa ni fa ba sai a fage yaki ake samun cin zarafin mata da kananan yara ba, akwai mata da ’ya’ya mata dake fuskantar cin zarafi maimakon kasancewa cikin aminci a gidajen su.”

Na tambayi Aisha Sunusi Sharfadi, Malama a Sashin Nazarin Zaman takewar Bil-adama dake Jami’ar Bayero ko ta wadanne hanyoyi ne al’adu ke ingiza cin zarafin mata a Najeriya?

“Al’adu ma gaskiya suna ta’azzara wannan cin zarafi da ake yiwa mata a gidan mazaje. Na farko za ka ga daman a al`adar mace dole ta yi biyayya ga mijinta a gidan aure koda mijin ya yi miki laifi sai dai ki ba shi hakuri ko da kuwa ke ce da gaskiya. Al`adar Bahaushe ya rene mu mu mata da halayyar hakuri da juriya. Babu batun barin gidan miji koda kin gudo zuwa gidan ku wata za ka ga iyayenta da kansu za su maida ita gidan mijin, wata ma ba za a lallashe ta, wata fada za a yi mata a ce ta gaggauta komawa gidan mijinta.”

To ko ta’azarar cin zarfin mata da kananan yara  na da alaka da talauci?

“Eh wasu matan ba za su iya komawa gidan iyayensu ba idan sun samu sabani da mazajensu, saboda yanayin talaucin da iyayen nasu ke ciki. Domin wasu in sun koma gidajen iyayen nasu babu wadataccen dakin da za su zauna, sanann babu isasshen abinci da za a iya ciyar da ita, dole sai dai ta yi hakurin zama a gidan mijin nata tare da yin hakurin da cin zarafin da zai yi mata.”

Da yake lamarin cin zarafi, batu ne na hakkin bil adama, Dr Lubabatu Dankade, shugabar Sashin Nazarin Sharia dake da alaka da Kasuwanci da dai-daikun mutane na Jami’ar Bayero a jihar Kano dake arewacin Najeriya kuma daya ce daga cikin kwarraru kan lamarin mata da yara kanana, na tambaye ta ko ina mafita ta fuskar shari’a?

“Abubuwa da ya kamata a yi su akwai wanda gwamnati za ta shigo, akwai kuma wanda mu kan mu mata za mu shigo. Ka ga kamar yadda na fada rashin ilimi, gwamnati tana ciki ke kanki ’ya mace kina ciki. Mata mu fita mu nemi ilimi, ita kuma gwamnati ta wayar da kan jama’a game da batun bayar da fifiko ga ilimin ’ya’yan mata. Muddin aka yi ilimi za a samu rangwame sosai. Na biyu kuma akwai wasu sassa a kundin dokokin kasa na 2015 da suka haramta cin zarafin ’ya’ya mata a Najeriya.”

Tun a shekrar 1983 ne, Majalisar Dinkin Duniya ta kaddamar da matakin kawo karshen Cin Zarafin Mata da Diya Mace, sai dai tun bayan kaddamar da matakin ne, Kungiyoyin Fararen Hula masu Rajin kare Hakkin Mata da kananan Yara ke cewa suna yin duk mai yuwa domin kawo karshen matsalar.  (Garba Abdullahi Bagwai)