logo

HAUSA

Qatar 2022: Argentina ta kai wasan karshe bayan ta doke Croatia da ci 3 da nema

2022-12-14 11:42:48 CMG HAUSA

 

A wasan dab da na karshe, na gasar cin kofin kwallon kafa na duniya dake gudana yanzu haka a kasar Qatar, kasar Argentina ta doke Croatia da ci 3 da nema, kuma da wannan sakamako Argentina ta kai wasan karshe na gasar.

Tun kafin tafiya hutun rabin lokaci ne Lionel Messi, ya jefa kwallon farko a ragar Croatia ta bugun daga kai sai mai tsaron gida, wadda ta kasance kwallo ta 5 da ya ci a gasar ta kasar Qatar. Ya zuwa yanzu yawan kwallayen da ya ci sun yi daidai da na Kylian Mbappé na kasar Faransa, inda su biyun ke kan gaba wajen zura kwallaye a gasar ta wannan karo.

Haka kuma, kwallon da Messi ya ci a wasan, ita ce ta 11, a jerin kwallayen da ci a gasannin cin kofin duniya da ya halarta, inda ya zarce Gabriel Omar Batistuta a wannan fage. Messi ya zama dan wasan kwallon kafar Argentina mafi yawan cin kwallaye a gasar cin kofin duniya.

Messi ya taimakawa Julián Álvarez wajen zura kwallo ta biyu a ragar Croatia, kafin daga bisani ya sake taimaka masa wajen jefa kwallo ta 3.  (Tasallah Yuan)